Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, a ranar Juma'a ya bayyana cewa domin adalci, ya kamata mulki ya koma kudu a shekarar 2023.
Ya soki maganganun cewa idan aka baiwa wani sashen kasar nan mulki zasu yi kokarin ballewa daga kasar.
Ya jaddada cewa akwai bukatar nuna adalci, saboda mayar da wani bangare saniyar ware ya sa suke neman ballewa daga kasa.
A jawabin da ya gabatar ranar Juma'a a Legas wajen taron tunawa da Cif Gani Fawehinmi, gwamna Zulum ya ce daya daga cikin hanyoyin da za'a samu cigaba a Najeriya shine nunawa ko wani bangare adalci.
Zulum yace:
"Na yarda cewa a baiwa wasu bangarori damar shugabantar kasar nan a 2023."
0 Comments