Wani lamari da a baya-bayan nan ya karaɗe shafukan sada zumunta musamman Tuwita shi ne ɓullar wata sabuwar ƙungiya ta maza marowata da a Turancin Ingilishi ake kira da Stingy Men Association of Nigeria.

Wannan dai ya sa ana ta tafka muhawara a shafukan da har aka ƙirƙiri maudu'in #stingymenasoociationofNigeria wanda ya samu karɓuwa a shafukan Facebook da Tuwita ɗin.

Sai dai batun na ci gaba da faɗaɗa inda ko a Kano, ake tafka mahawara tsakanin samari da ƴan mata kan ƙungiyar samari masu matse bakin aljihu ko masu dunƙule hannu da ya zuwa yanzu take da mabiya sama da dubu 120.  

Matasan masu dunƙule hannu sun ce sun kafa ƙungiyar ne don kawo ƙarshen yaudarar 'yan mata, waɗanda suka mayar da su saniyar tatsa.

Dalilin kafa Qungiyar

A cewar Umar Faruk Al-ikhwani, maƙasudin ƙirƙirar ita wannan ƙungiya na da nasaba da matsalolin da matasa suke fuskanta da kuma yadda mata suke jibga musu ɗawainiyarsu.

Ya ce za ka ga "yarinya ta tara samari sama da biyar kuma kowanne akwai hidimar da take buƙata ya yi mata, misali za ka ga yarinya tana da ƙawaye da aka yi musu aure da samari kuma kowanne ta tsara wane shi zai yi mata ankon wance".

Ya bayyana cewa manufar ƙungiyar ita ce yaƙi da yaudara ka ga ke nan idan aka magance buɗe bakin aljihu zai zama an saita ƴan matan ta yadda za su tsaya da saurayi ɗaya.

Sai dai Hafsa Aliyu ta ce akwai son zuciya a yadda samarin suka haɗu suka kafa ƙungiyar saboda a ganinta, "idan kana son mutum da gaske, sadakin so shi ne kyauta don ka yi wa abin da kake so kyauta wannan ba laifi bane".

Ta ce ƙungiyar ta ɓullo da wani salo na rowa ne saboda a tsarin rayuwa, duk wanda za ka zauna da shi "kana buƙatar ka more shi ya more ka" wanda Al-ikhwani ya ce sam ƙungiyar ba ta nemi matasa su yi rowa ba illa dai tana nemansu ne su saita bakin aljihu ta yadda za su tunkari yarinyar da suke son aura da kyakkyawar manufa.