Hamshakin mai kudin duniya, Elon Musk, ya tafka asarar $14 biliyan a rana daya

Babban mai arzikin duniya na makon jiya ya tafka babbar asara a ranar Alhamis

Ya rasa gagarumar dukiya da ta kai dala biliyan 14, lamarin da ya matukar girgiza dukiyarsa.
A halin yanzu Jeff Bezos mai Amazon ne ya zama mutum mafi arziki a fadin duniya

Elon Musk ya sauka daga inda yake a jerin manyan masu kudin duniya. A makon da ya gabata ne aka bayyana shi a matsayin mutumin da yafi kowa kudi a duniya.
Amma kuma a rana daya ya sauka daga wannan matsayin bayan tafka asarar dala biliyan 14 da yayi, shafin Linda Ikeji ya wallafa.

A halin yanzu biloniya Tesla ne zama mutum na biyu da yafi kowa kudi a fadin duniyar nan.

Hannun jarinsa na bangaren hada motoci da ke aiki da wutar lantarki ya fadi da kashi 8 a ranar Litinin, 8 ga watan Janairun 2021, lamarin da ya tura Muska kasa da dala biliyan 176.2.

A cikin kankanin lokacin, mamallakin Amazon, Jeff Bezos ya zama mutumin da yafi kowa kudi a duniya kamar yadda Forbes ta kiyasta.

A halin yanzu yana kasan Bezos da dala biliyan 6 kuma dukkan dukiyarsa a halin yanzu dala biliyan 182.1 ce.

Duniya juyi juyi